1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Abiy Ahmed na neman hadin kan al'umma

Abdourahamane Hassane
June 16, 2021

Firaministan Habasha Abiy Ahmed ya yi  kiran da a samar da hadin kai da zaman lafiya mai dorewa a kasarsa tare da kawo karshen rigingimu na siyasa da yake-yake tsakanin kabilu.

https://p.dw.com/p/3v3pD
Äthiopien Ministerpräsident Abiy Ahmed Ali
Hoto: Office of the Prime Minister/Reuters

Aby Ahmed da ke  magana a Jimma mahaifarsa da ke a yankin Oromia a arewacin kasar a farfagandinsa a rana ta karshe ta kampe kafin zaben 'yan majalisar dokokin da za a yi a ranar 21 ga watan Yuni(21-06-21), ya ce yin haka shi ne wajibi. Zaben na 'yan majalisun dokoki wanda aka shirya yi tun a cikin watan Augusta na shekara ta 2020 an dageshi har' sau biyu saboda corona abin da ya janyo tayar da kayar baya na 'yan yankin Tigray da suka nemi balewa.