1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kashe ɗan uwan shugaban Afghanistan

July 12, 2011

Masu tsananin kishin addinin musulunci sun kashe Ahmed Wali Karzai,ɗan uwan shugaban Afghanistan Hamid Karzai a birnin Kandahar a daidai lokacin da shugaba Nicolas Sarkozy na Faransa ya kai ziyarar ba zata a wannan ƙasa.

https://p.dw.com/p/11teQ
Marigayi Ahmed Wali Karzai, ɗan uwan shugaban AfghanistanHoto: AP

'Yan ƙungiyar taliban na Afghanistan sun hallaka ɗan uwan shugaba Hamid Karzai, a daidai lokacin da Faransa ta sanar da aniyarta ta janye dakarunta dubu huɗu daga ƙasar a ƙarshen shekara mai zuwa. Shi dai Ahmed Wali Karzai, an kashe shi ne a gidansa da ke birnin Kandahar a wannan talata, yayin da shugaban na Afghanistan ke shirin ganawa da takwaran aikinsa na Faransa wato Nicolas Sarkozy da ya kai ziyarar bazata a ƙasar.

Ahmed Wali Karzai da ake zargi da cin hanci da karɓar rashawa, da kuma safarar miyagun kwayoyin, ya na daga cikin waɗanda suke taimaka wa shugaba Karzai samun angizo a yankin Kandahar da ke fama da ayyukan ta'addanci. Shi dai Sarkozy da ya tattauna da dakarun Faransa da ke jibge a Surobi da ke arewa maso yammacin birnin Kaboul, shi ne shugaban na uku baya ga na Amirka da kuma na Birtaniya da ya tabbatar da janye sojojin ƙasarsa daga Afghnaistan.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Umaru Aliyu