An kashe Yasser Arafat da plonium 210 | Labarai | DW | 06.11.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kashe Yasser Arafat da plonium 210

Sakamakon bincike na farko da ƙwararru na ƙasar Switzerland suka gudanar ya nuna cewar an yi amfani da gubar plonium 210 wajen kashe tsohon jagoran na Palasɗinawa.

Gidan telebijan na Al-Jazeera wanda shi ne ya bayyana labarin, ya ce ɗaya daga cikin ƙwararrun ya shaida cewar, sun gano haka ne bayan gwaje-gwajen da suka yi a kan tshoffin kayayyakin da tsohon shugaban ya yi zaman yin amfani da su. Irin su magogin baƙi da kayan kwana da dai sauransu.

Arafat ya mutu yana da shekaru 75 a cikin watan Nuwamba na shekara ta 2004.Daman dai tun a shekara bara ne ƙwararru suka tono gawar tsohon shugaban a Ramallah inda aka bizneshi domin ɗibar wasu sassan jikinsa don yin gwaje-gwajen na ƙasussuwa da sauransu.

Mawalafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Saleh Umar Saleh