SiyasaAfirka
An kashe wasu yan kunar bakin wake na Al-Shabaab a Mogadishu
October 5, 2025
Talla
Ma'aikatar Cikin Gida a Somaliya ta fitar da sanarwar cewa ta yi nasarar halaka 'yan kunar bakin waken, a kusa da gidan yarin Godka Jilicow da ake ajiye mayakan kungiyar Al-Shabaab da aka cafke kafin a gurfanar da su a gaban kuliya.
Karin bayani: Mutane 8 sun mutu a hare-hare a Somaliya
Somaliya na fama da tashe-tashen hankulan mayaka masu ikirarin jihadi wadanda kuma ke da alaka da kungiyar Al-Qaeda. Duk da kalubalen da kasar ke fuskanta na rashin tabbas ta fuskar tsaro da tattalin arziki Shugaba Hassan Sheikh Mohamud ya shirye gudanar da zabe a 2026.