1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kashe wasu 'yan jarida a Haiti

January 7, 2022

Rahotanni daga kasar Haiti na nuni da cewa wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun kashe 'yan jarida biyu a kusa da babban birnin kasar Port-au-Prince. 

https://p.dw.com/p/45F44
World Press Freedom Day | Haiti 2002
Hoto: Thony Belizaire/AFP/epa/dpa/picture-alliance

Dan jaridan na uku ya sami nasarar tserewa daga yankin na Laboule 12, inda ake kashe abokan aikin nasa. Gidan radion Ecoute FM, inda guda daga cikin 'yan jaridar da aka kashe ke aiki ya bayyana kisan a matsayin zalunci.

Ana dai ganin yankin na Laboule 12 a matsayin wurin da ake tafka kazamin fada tsakanin kungiyoyin 'yan bindiga da ke neman iko.

Har yanzu ba a samun nasara a bincike da dama musamman na kisan 'yan jarida da ake gudanarwa ba. Kasar Haiti ta kuma fadawa cikin rikicin siyasa tun bayan kashe tsohon shugaban kasar Jovenel Moise a gidansa da ke babban birnin kasar.