An kashe wasu sojoji a Sudan
July 14, 2013Talla
Wani kakakin rundunar ta haɗin gwiwa tsakanin Tarrayar Afirka da Majalisar Ɗinkin Duniya, ya ce wasu yan bindigar ne suka yi wa sojojin kwanton ɓauna, suka kuma buɗe masu wuta a lokacin da suke yin sintiri a yanki.
Masu aiko da rahotannin sun ce yawanci sojojin da lamarin ya rutsa da su 'yan ƙasar Tanzaniya ne. Biyu daga cikin mutane 17 da suka jikata mata ne, kuma babban sakataran MMD Ban-Ki -Moon ya yi Allah Wadai da harin. Wannan dai ita ce asara ma fi muni da rundunar ta samu na sojojinta tun shekaru biyar da kafata a Sudan.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Zainab Mohammed Abubakar