An kashe wasu mutane a gabashin Kwango | Labarai | DW | 07.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kashe wasu mutane a gabashin Kwango

Rahotanni daga birnin Goma na Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango na cewa, 'yan tawayan kasar Uganda sun hallaka mutane kalla 36 a yankin gabashin kasar.

Wannan sabon kashe-kashen gilla da aka dora alhakin sa kan 'yan tawayan kasar Uganda, ya kai adadin wadanda suka mutu sakamakon hare-haren ga mutun 250 idan aka hada da na garin Beni da ke yankin arewacin Kivu daga farkon watan Oktoban da ya gabata kawo yanzu.

A daren Asabar ne wayewar wannan Lahadi, 'yan tawayan da ake zargi na Uganda suka aikata wannan sabon kisan gillar a garin Oicha da kuma wasu garuruwa biyu da ke kewaye da wannan gari, inda a cewar Kanar Celestin Ngeleka kakakin dakarun kasar ta Kwango na Operation Sokola1 masu fafutukar yakar 'yan ta'adda a yankin gabashin kasar, ya ce bayan sun gudanar da binciken neman gawawakin ne suka samu wannan adadi na mutane 36 da aka kashe sabanin 14 da suka bayyana da farko.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Pinado Abdu Waba