An kashe wani sojin Majalisar Ɗinkin Duniya a Mali
August 16, 2014Talla
Masu yin jahadin sun kai harin ne da wata motar da ke maƙare da abubuwan da ke fashewa a harabar rundunar ta wanzar da zaman lafiya ta MINUSMA da ke a garin Ber wanda ke da nisan kilomita 60 daga birnin Timbuktu.
Yawancin dakarun da ke cikin wannan runduna dai 'yan ƙasar Burkina Faso ne. Mayaƙan masu kaifin kishin addini waɗanda suka mamaye arewacin Mali tun a shekarun 2012 kafin daga bisanin dakarun ƙasashen duniya su koresu,sun daɗa kai hare-hare a Mali a 'yan kwanakin baya-baya nan.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Zainab Mohammed Abubakar