An kashe wani matashi a zanga zangar Bahrain. | Labarai | DW | 14.02.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kashe wani matashi a zanga zangar Bahrain.

An harbe Matashin ne har lahira a lokacin wata zanga-zanga domin cika shekaru biyu da bore da jama'ar ƙasar suka gudanar domin samun sauye sauye na siyasa.

An sha arangama tsakanin yan sanda da duban jama'a da ke yin zanga zanga a cikin wasu garuruwa da yan shi'a ke da rinjaye;domin tunawa da juyin juya halin da bai samu nasara ba.

Jama'ar sun yi zanga zangar ce; a wani amsa kiran yajin aikin gama gari da suka yi daga wata ƙungiar yan adawa.Ministan cikin gida na ƙasar ya sanar da cewar masu zanga zanga sun datse hanyoyi da dama na birni Manama da shingaye.Wanda a lokacin da jami'an tsaro suke ƙokarin cire su ;yaron ya samu rauni.Yan ɗarikar Sunni wanda suke riƙe da mulkin ƙasar, a shekara 2011 sun fatataki masu zanga zangar da ke neman sauye sauye wanda a ciki mutane guda tamanin suka mutu.

Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Mohammad Nasiru Awal