An kashe wani jami′n Red Cross a Afirka ta Tsakiya | Labarai | DW | 21.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kashe wani jami'n Red Cross a Afirka ta Tsakiya

Mjiyoyin kiwon lafiya sun ce an kashe mutane guda biyar tare da wani jami'in Ƙungiyar agaji ta Red Cross kana aka raunata wasu guda goma a birnin Bangui.

Hakan ya biyo bayan faɗan da ake fafatawa tun ranar Talata tsakanin dakarun ƙawance na ƙasashen duniya da ƙungiyoyin mayaƙa da ke ɗauke makamai.

Wani jami'in kiwon lafiya na asibitin birnin Bangui ya ce addadin mutanre da suka mutu zai iya ƙaruwa, saboda akwai wasu musulmi da aka harba da bindiga waɗanda ba a san cikin halin da suke ba kawo yanzu. Ƙungiyar agaji ta Red Cross ta ce an kashe jami'in ne a lokacin da yake ƙoƙarin ba da agaji ga wani wanda ya samu rauni a shiyar PK5 da ke a birnin na Bangui inda musulmi ke da rinjaye.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu