An kashe sojojin kiyaye zaman lafiya a Kwango | Labarai | DW | 10.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kashe sojojin kiyaye zaman lafiya a Kwango

Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah wadai da harin da ya kashe sojojinta biyu tare da jikkata wasu 18 a gabashin kasar Kwango, hukumomin kasar na zargin mayakan kungiyar ADF ta Uganda da kai harin.

Mai magana a madadin ofishin Majalisar Dinkin Duniya a kasar Kwango Florence Marchal, da ya ke tabbatar da harin ya kuma ce 'yan bindigan sun kwace manyan makamai a yayin da suka sammaci sojojin kiyaye zaman zaman lafiya da ke a gabashin kasar.

Wannan harin dai na zuwa ne kwana guda bayan da 'yan tawayen na Uganda, suka kai wani hari da ya kashe fararen hula akalla 10, yayin da wasu sama da 20 suka yi batan dabo a kusa da garin Beni.

Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya  António Guterres, ya umarci mahukuntan jamhuriyar dimokradiyar Kwango da su gagauta bincike dan gabatar da maharan a gaban shari'a, Guterres ya kuma gargadi gwamnatin Kwango da su dau matakan gaggauwa na takaita kai hare-hare a kan sojojin kiyaye zaman lafiya da ke kasar, a cewarsa rashin yin haka ka iya zama laifukan yaki da ya saba dokokin kasa da kasa.