An kashe mutane da dama a birnin Bangui | Labarai | DW | 27.12.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kashe mutane da dama a birnin Bangui

Ƙungiyar agaji ta Red Cross ta ce ta tsintsi gawarwakin mutane guda 40 a kan tittunan Bangui babban birnin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Wani kakakin ƙungiyar daga Jeniva David Pierre Marquet ya ce yawanci waɗanda lamarin ya rutsa da su an yi amfani da makaman gargajiya wajen kashe su,sannan ya yi gargaɗin cewar addadin waɗanda suka mutu zai iya ƙaruwa saboda a halin da ake ciki a kwai unguwanin da jami'an agaji ba zasu iya kutsa kai.

Ɗarurruwan mutane dai na ta tserwa daga birnin Bangui tun jiya,lokacin da sojojin sa kai kirista suka kashe sojoji Chadi guda shida waɗanda suke zargi da goyon bayan 'yan ƙungiyar SELEKA musulumi.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane

Edita : Umaru Aliyu