An kashe mutane a ƙalla 185 a Najeriya
April 22, 2013An bada rahoton cewa mutane sama da 150 suka mutu a sanadin faɗan. Masu aiko da rahotanni sun ce an kwashe awoyi ana yin bata kashi tsakanin maharan da sojojin abin da ya tilasta wa mutane da yawa tserewa daga yankin.
Kuma baya ga asarar rayukan jama'a da aka samu, an ƙona gidaje da motoci da kuma kamfanoni da dama. Wani wanda ya gane wa idonsa abin da ya faru ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Faransa AFP, cewar hukumomin yankin sun binne gawarwakin mutane a ƙalla 185 a ranar Lahadi. Wannan al'amari ya faru ne a daidai lokacin da gwamnatin Tarrayar Najeriya ta ba da sanarwar girka wani kwamiti, wanda zai tattauna batun yin afuwa ga 'yan ƙungiyar Boko Haram domin samar da zaman lafiya a Najeriyar.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mohammad Nasiru Awal