An kashe mutane 40 a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya | Labarai | DW | 21.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kashe mutane 40 a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Rahotanni daga Jamhuriyar Afirka ta Tsakiyya na cewar addadin wadanda suka mutu a fadan da aka gwbza a garin Bria da ke a yankin tsakiyya na kasar ya kai mutun 40.

Tashin hankalin  wanda aka kwashe tsawon yinin jiya ana yi tsakanin Kiristoci na Antibala da Musulmi na Kungiyar Seleka. Ya faru ne a dai dai lokacin da aka cimma wata yarjrjenia a birnin Roma na Italiya tsakanin bangarorin 'yan tawayen da kuma gwamatin da ke yin gaba da juna wanda Cocin Roman Katolika ya shiga tsakani, don kawo karshen tashin hankalin da aka kwashe dogon lokaci ana yi a Jamhuriyar ta Afirka ta Tsakiya