An kashe mayakan al-Shabaab 100 a Somaliya | Labarai | DW | 21.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kashe mayakan al-Shabaab 100 a Somaliya

Jiragen yakin Amirka sun yi nasara kan mayakan, a wani somame da suka kaddamar a sansanonin kungiyar da ke da nisan kilomita 200 da babban birin kasar Mogadishu.

A wata sanarwa da rundunar sojojin Amirka suka fitar, na cewa harin na hadin gwiwa ne da ya samu goyon bayan dakarun gwamnatin Samaliya a yunkurin kakkabe 'yan tawaye da ke barazana da rayuwar fararen hula da sojoji a Somaliya.

Sanarwar ta ce za a ci gaba da kai farmaki kan mafakar mayakan a duk inda suke a fadin kasar, Amirka dai na ci gaba da kaddamar da jerin hare-hare kan kungiyar al-Shabaab a cikin wannan shekara da nufin tabbatar da alkawuran shugaban Amirka Donald Trump na kakkabe tsagerun kungiyoyi masu tsauraran akidu a gabashin Afirka.