An kashe masu zanga-zanga a Masar | Labarai | DW | 29.03.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kashe masu zanga-zanga a Masar

Mutane aƙalla guda biyar aka kashe a birnin Alƙahira a lokacin wani yamutsin da magoya bayan Ƙungiyar 'Yan Uwa Musulmi suka gudanar.

Ofishin ministan cikin gida na ƙasar Masar ya ce aƘalla mutane guda biyar aka kashe a birnin alƙahira a sakamakon arangamar da aka sha tsakanin magoya bayan Ƙungiyar 'Yan Ua Musulmi da ke yin zanga-zangar da kuma jami'an tsaro.

Masu aiko da rahotannin sun ce a cikin waɗanda aka kashen har'da wata 'yar jarida Mayada Ashraf ta jaridar Alnusura wacce ta gamu da ajalinta a fagen daga a lokacin da take yin aikin ɗaukar rahotanni a kan zanga-zangar. Magoya bayan hamɓararran shugaban ƙasar wato Mohammed Mursi sun gudanar da zanga-zangar ne, domin nuna adawa da hukuncin kisan da aka yankewa wasu magoya bayan ƙungiyar kusan ɗari biyar. Gwamnatin dai ta ce ta kama mutane 73 a duk faɗin ƙasar waɗanda take zargi da yin amfanin da makamai a wajen zanga-zangar.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe