An kashe masu zanga-zanga a Masar | Labarai | DW | 26.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kashe masu zanga-zanga a Masar

An ba da rahoton cewar an sha arragama tsakanin magoya bayan Muhammad Mursi tsohon shugaban ƙasar da masu yin adawa da shi.

A birnin Alexandriya da ke a yankin arewacin ƙasar an kashe mutane guda biyu a fadan da aka gwabza tsakanin sassan biyu. Nadiya El Abbas wata mai goyon bayan Mursi ce da ta halarci gangamin daga yankin arewacin ƙasar.

Ta ce : ''Mun zo ne nan, domin nuna goyon baya ga cikkaken shugaba,ta ce ba za mu amince da wani shugaba ba,domin Mursi shi ne shugaban da muka zaɓa.'' A share ɗaya kuma masu neman sauyi sun riƙa raira kallamun nuna ƙemar tsohuwar gwamnatin tare da jinjinawa hukumomin sojin da suka yi juyin mulki.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Zainab Mohammed Abubakar