An kashe daliban firamare uku a jihar Borno | Labarai | DW | 30.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kashe daliban firamare uku a jihar Borno

A Najeriya wani mutun ya kai hari da adda a wata makarantar firamare a wani gari na Kudu maso Yammacin jihar Borno inda ya halaka wasu daliban makarantar guda uku 'yan shekaru biyar zuwa takwas da haifuwa. 

Rahotanni daga Najeriya na cewa wani mutun ya kai hari da adda a wata makarantar firamare a wani kauyen jihar Borno inda ya halaka wasu daliban makarantar guda uku 'yan shekaru biyar zuwa takwas da haifuwa. 

Kamfanin dillancin labaran Farsansa na AFP ya ruwaito Habibu Suleiman wani mazaunin garin na cewa da misalin karfe tara da rabi na safiyar wannan Alhamis ce mutuman ya kutsa a cikin ajujuwan renon yara na makarantar firamaren Jafi inda nan take ya kashe dalibai biyu 'yan shekaru biyar da kuma bakwai ta hanyar fasa masu kai da addar.

Dalibi na uku wata yarinya ce 'yar shekaru takwas wacce ta rasu lokacin da ake kan hanyar kaita assibiti bayan da maharin ya datsa mata adda a hanci. Kazalika mutuman ya jikkata malamar daliban a lokacin da ta yi yinkurin kare yaran, kafin daga karshe ma'aikatan makarantar su yi nasarar murkushe shi. Yanzu haka dai mahukuntan jihar Borno sun sanar da rufe makrantun kauyen da aka kai harin a bisa fargabar sake fuskantar wani sabon harin.