An kashe Abu Musab Alzarqawi | Labarai | DW | 08.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kashe Abu Musab Alzarqawi

Firaministan kasar Iraqi Nouri al-Maliki ya sanarda cewa sojojin Amurka sun kashe shugaban kungiyar Alqaeda na kasar Iraqi Abu musab alzarqawi cikin wani harin jiragen sama da aka kai a wurin da yake boye.

Firaministan yace an kuma kashe wasu na hannun damansa 7 cikin wannan hari na daren jiya kusa da garin Baquba,wadda ke da tazarar kilomita 65 daga arwacin birnin Bagadaza.

Babban komandan rundunar sojin Amurka a Iraqi ya fadawa manema labari cewa an tabbatar da cewa alzarkawai aka kashe cikin wannan hari.

Wani jamiin kasar jordan yace kasarsa ta taimaka wajen bada bayanan gano inda alzarqwawi yake boye.

Yan kungiyar ta alqeda a Iraqi sun aike da sako ta yanar gizo wanda ya tabbatar da kashe shugaban nasu,inda kuma suka lashi takobin ramuwar gaiya ga abinda suka kira shahada da yayi.