An kara yin kira ga Firaministan Hungary Gyurcsany da ya yi murabus | Labarai | DW | 19.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kara yin kira ga Firaministan Hungary Gyurcsany da ya yi murabus

Dubun dubatan masu zanga-zanga sun yi gangami a gaban ginin majalisar dokokin kasar Hungary dake birnin Budapest suna neman FM Ferenc Gyurcsany da yayi murabus. Da farko wani gungun masu zanga zanga sun farma ofisoshin tashar telebijin ta kasa inda suka hana ta watsa shirye shiryenta. Wannan tashin-tashinar ta zo ne bayan buga wani faifayen rekoda dake dauke da muryar FM ya na amsa cewa gwamnati ta shara karya game da matsayin tattalin arzikin kasar don lashe zaben da aka gudanar a cikin watan afrilu. Yayin da jam´iyar ´yan gurguzu ke marawa FM baya a wannan kalubale mafi girma dake yake fuskanta tun bayan darewarsa kan mulki a shekara ta 2004, su kuwa ´yan adawa kira suke yi a gareshi da yayi murabus. Tuni kuwa shugaban kasar Hungary ya ce FM Gyurcsany ya jefa tsarin demukiradiya a kasar cikin hadari.