Kara wa'adin dakarun kiyaye zaman lafiya a Mali
June 28, 2019Talla
Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da kara tsawon waA'din dakarun kiyaye zaman lafiya na majalisar da ke kasar Mali. Kwamitin ya ce yanayin da ake cikin a watanni shida da suka gabata na tashe-tashen hankula suka janyo amincewa da kara zaman sojojin kasashen duniya har zuwa karshen watan Yuni na shekara mai zuwa ta 2020, inda aka kara wa'adin da tsawon shekara guda.
Gaba daya mambobin Kwamitin Sulhun na Majalisar Dinkin Duniya suka amince da wannan mataki. Francois Delattre ke zama jakadan Faransa a Majalisar Dinkin Duniya wanda ya nuna gamsuwa da wannan mataki.