An kammala zaɓuka a ƙasar Kamarun
September 30, 2013A ƙasar Kamarun ranar Litinin ɗinnan aka gudanar da zaɓen 'yan majalisar dokoki da na ƙananan hukumomi, inda ake ganin jam'iyyar CPDM ko kuma RDPC da ke mulkin ƙasar tun samun yancin kai, babu ɗaya biyu sai ta karkata sakamakon don ta yi nasara. Shugaba Paul Biya ɗan shekaru 80 da haifuwa tun sama da shekaru 30 ya ke kan mulki, a bariya ya sake lashe zaɓe shugabancin kasar, kuma sau uku yana ɗage zaɓen 'yan majalisar dokokin, a wani abin da yan adawa suka ce duk hanya ce ta yadda zai tabbatar ya birkita al'amura, domin jam'iyyarsa ta ci gaba da kasancewa da rinjaye a majalisar dokoki. Babbar jam'iyyar adawa ta Social Demokrat wato SDF, ita ce ke bi a baya, kana akwai wasu ƙananan jam'iyyu 41 da ke fafatawa kan kujeru 180.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Mouhamadou Awal