An kammala shirye-shiryen zaben kasar Mali | Labarai | DW | 27.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kammala shirye-shiryen zaben kasar Mali

A ranar Lahadi ake sa ran miliyoyyin 'yan kasar Mali za su zabi sabon shugaban kasa.

A ranar Lahadi miliyoyin 'yan kasar Mali za su gudanar da zaben shugaban kasa-abin da ake sa ran zai kawo karshen rikicin siyasa na watanni 18 da ya kai fafatawa da kungiyoyi masu dauke da makamai.

'Yan takara 27 da ke neman kujerar shugabancin kasar sun kwashe makonni uku suna yakin neman zabe cikin lungu da sakon kasar. A ranar Jumma'a aka kawo karshen yakin neman zabe, kuma babu wani tashin hankalin da aka samu.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban ki-moon da shugaban gwamnatin rikon kwaryar kasar ta Mali,Dioncounda Traore, duk sun amince da kalubalen da kasar ke fuskanta, sannan suka nemi 'yan kasar ta Mali su mutunta sakamakon zaben.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Halima Balaraba Abbas