An kammala hawan Arafat
November 15, 2010Musulmi kimanin miliyan uku sun hallara a filin Arafat a yau Litinin domin gudanar da ɗaya daga cikin muhimman ayyukan ibada na Hajji. Hawa dutsen Arafat dai na zama ƙololuwar aikin Hajji a kowace shekara a ranar tara ga watan zulhaji.
Ma'aikatar cikin gidan Saudiya ta ce a bana Musulimi kimanin miliyan 1.7 daga ƙasashen duniya 181 suka shiga daular ta ƙasa mai tsarki domin gudanar da wannan ibada dake zama ɗaya daga cikin shika-shikan addinin Musulunci guda biyar.
An dai tsaurara matakan tsaro ga aikin na hawan Arafat da yanzu haka aka kammala
Mohammed Baki wani dan kasar Siriya na daga cikin rukunin jamaar da suka yi aikin hajin.
Yace abin farin ciki ne mafi misali a wannan rana da Allah ya bamu iko aikata wadanan ayyuka na alheri domin samun rahamar Allah da kuma neman gafartarsa. .
Mawallafi : Abdurahaman Hassane
Edita : Abdullahi Tanko Bala