An kame 'yan Amhara da dama a Habasha
June 27, 2019Talla
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito wani kusa a jam’iyyar ta Amhara na cewa a Addis Ababa babban birnin kasar ta Habasha kawai, jami’an tsaro sun kama fiye da mutun 50 daukacinsu magoya bayan jam’iyyar da suka zarga da yunkurin kifar da gwamnatin, kana kuma hatta ma a yankin Oromo ma akwai wasu tarin gwamman magoya bayan jam’iyyar da aka damke bisa wannan yunkuri.
A karshen makon jiya ne dai hukumomi a kasar suka ambaci wani yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba, to amma kuma ya yi sanadiyar mutuwar shugaban hafsan hafsoshin soja na kasar ta Habasha.