An kame shugaban yan tawayen Hutu | Labarai | DW | 09.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kame shugaban yan tawayen Hutu

Rundunar yan sanda a nan Jamus sun kame shugaban kungiyar yan tawayen Hutu Ignace Murwana Shyanka garin Mannheim dake kudu maso yammacin Jamus. Maiáikatar alámuran cikin gida ta nan Jamsu ta ce Murwan Shyanka wanda ya shafe shekaru goma sha biyar yana zaune a nan Jamus na daga cikin mutane goma sha biyar da kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ya bada sammaci domin a kamo su. Kungiyar yan tawayen Hutu ta FDLR wadda ke da mazaunin ta a kasar Congo ana zargin ta hannu a kisan kiyashin da aka yiwa yan kabilar tutsi su kimanin 800,000 a yakin basasar kasar Rwanda.