An kame masu adawa da tazarcen Kabila | Labarai | DW | 10.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kame masu adawa da tazarcen Kabila

'Yan siyasa takaws da suka yi canjin sheka daga bangaren gwamnatin Kwango i zuwa bangaren adawa ne suka shgia hannu 'yan sanda a Lubumbashi.

Sojojin Jamhuriyar Demokaradiyar Kwango sun kame wasu 'yan adawa takwas a Lubumbashi babban birnin jihar Katanga bisa zarginsu da haddasa gobara a cibiyar jam'iyyarsu ta Unafec. Sai dai kuma magoya bayansu sun danganta wannan mataki da bita da kullin gwamnatin Kabila, saboda sauyin sheka da 'yan siyasan suka yi zuwa ga bangaren adawa.

Wadanda suka shaidar da kamen suka ce jami'a tsaron sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa mutane da suka taru a cibiyar jam'iyyar ta Unafec, lamarin da ya jikata mutane da dama.

'Yan adawan na Kwango na daga cikin wadanda suka gargadi shugaba Joseph Kabila da ka da ya kwaskware kundin tsarin mulki domin gudanar da wa'adin mulki na uku. Sai dai kuma shugaban na Kwango na shirin gudanar da babban taron kasa kan batun tazarce. Tuni ma aka fara sa-in-sa tsakanin masu goyon tazarce da kuma masu adawa da mulkin sai madi ka ture.