An kama wani fitaccen dan Al-Qaida a Jordan | Labarai | DW | 27.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kama wani fitaccen dan Al-Qaida a Jordan

Jami'an tsaro a kasar Jordan sun kama fitaccen jigon nan na kungiyar Al-Qaida Abu Mohammad al Maqdisi bisa zarginsa da tunzura mutane su yi aiyyukan ta'addanci.

Hukumomi suka ce sun kama al-Maqdisi din ne a wannan Litinin din bayan da aka gayyace shi domin amsa wasu tambayoyi a ofishin mai gabatar da kara na kasar. Yanzu haka dai jami'an tsaron sun ce za su cigaba da tsare shi har nan da kwanaki goma sha biyar da ke tafe.

Gabannin bayyana shirin nasu na tsare shi da, jami'an tsaron sun tuhume shi zargin amfani da intanet wajen nuna goyon baya da ma jan hankali mutane wajen karkata ga yin jihadi da kungiyoyi masu kaifin kishin addini ke da'awar yi.