An kama madagun ′yan adawan Uganda | Labarai | DW | 18.04.2011
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kama madagun 'yan adawan Uganda

'Yan sanda ba su bayyana dalilan tsafke ɗan adawa Kizza Besigye tare da tsare shi ba, amma kuma ba zai rasa nasaba da zanga-zangar nuna ɓacin rai game da tsadar rayuwa da za ta gudana wannan Litinin a Kampala ba.

Kizza Besigye lokacin tattaunawa da mai ɗakinsa

Kizza Besigye lokacin tattaunawa da mai ɗakinsa

'Yan sandan Uganda sun tsafke madugun 'yan adawan ƙasar wato Kizza Besigye da ke shirin halartar zanga-zangar nuna ƙosawa da tsadar rayuwa da za ta gudana a birnin Kampala. Babbar sakatare janar na jam'iyarsa wato Alice Alaso ta bayyana cewar jami'an na tsaro sun damƙeshi ne da jijjiɓin safiyar wannan Litinin a daidai lokacin da ya ke fitowa daga gidansa.

Su dai jami'an tsaro sun bayyana tartibin dalilan da ya sa suka tsafke shi, tare da tsare shi ba ba. Amma kuma suka ce kamen, ba shi da alaƙa da zanga-zangar nuna ƙosawa da hauhawar farashin kayan bukatun yau da kullum da ke tafe. Sai dai kuma, shi madagun 'yan adawan ya na daga cikin waɗanda suka ji rauni, a lokacin da 'yan sandan kwantar da tarzoma suka yi amfani da borkono mai sa hawaye da kuma harsasan roba wajen tarwatsa masu zanga-zanga a makon da ya gabata.

Ko da shi ke dai gwamnatin ta Uganda ta haramta wannan gangami, tare da barazanar far ma waɗanda za su fantsama kan tituna da sunan bore, amma kuma waɗanda suka yi kira da a gudanar da boren, suke ca babu gudu babu ja da baya.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Mohammad Nasiru Awal