1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kai wa sojoji hari a jihar Tahoua

Zulaiha Abubakar
December 10, 2019

Akalla sojoji biyu sun rasa rayukansu yayin da wasu biyar suka jikkata sakamakon hari da wasu mahara suka kai barinkin sojoji da ke Aghandau a yankin Tilliya a iyakar kasar Nijar da Mali .

https://p.dw.com/p/3UWPg
Nigeria Soldaten
Hoto: I. Sanogo/AFP/Getty Images

Wannan dai shi ne hari na biyu da aka kai a jihar ta Tahoua ta Jamhuriyar Nijar cikin kwanaki biyar. Ko a karshen makon jiya wasu mutane sun afka wa birnin Konni da ke kusa da iyakar Nijar da Najeriya, inda suka karbe kudade daga hannun wasu attajiran yankin.

Wani mazaunin yankin da sansanin sojojin yake ya bayyana wa wakilin DW cewar maharan sun rufe fuskokinsu cikin rawani kafin su kutso cikin yankin da misalin karfe biyu da rabi na daren jiya Litinin, kuma sun yi ta harbe-harbe tsakanin su da sojojin har kusan wayewar gari.

Yanzu haka dai al'umomin d ake zaune a kusa da iyakokin kasar na cikin fargaba.