An kai sabon harin ta′addanci a New York | Labarai | DW | 11.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kai sabon harin ta'addanci a New York

A kasar Amirka mutane uku ne suka jikkata a cikin wani harin ta'addanci da wani mutun ya kai a wata hanyar karkashin kasa ta birnin New York inda ya tayar da wani bam kirar gargajiya. 

A kasar Amirka mutane uku ne suka jikkata a cikin wani harin ta'addanci da wani mutun ya kai a wata hanyar karkashin kasa ta birnin New York inda ya tayar da wani bam kirar gargajiya. 

A wata fira da ya yi da manema labarai bayan afkuwar lamarin, magajin garin birnin na New York Bill de Blasio ya bayyana cewa wani mutun ne dan shekaru 27  mazaunin unguwar Brooklyn ya kai harin da misalin karfe 12 da mintocin 20 agogon JMT. JAMES O'NEILL, kwamishinan 'yan sanda na birnin New York ya yi karin haske kan lamarin yana mai cewa:

Ya ce "jami'anmu sun iske mutuman dan shekaru 27 mai suna Akayed Ullah ya jikkata inda bam din ya tashi, kuma binciken farko da muka gudanar ya nunar da cewa yana dauke da jigidar bam na gargajiya a jikinsa ne lokacin da ya tashi"

Bayan afkuwar lamarin 'yan sanda sun yi wa wajen zobe tare da datse wasu hanyoyin zirga-zirga jiragen kasa da na motoci. Tsohon kwamishinan 'yan sanda na birnin New York ya bayyana wa MSNBC cewa maharin dan asalin kasar Bangladesh ne kuma kai harin ne da sunan Kungiyar IS. ruwayar da ya zuwa yanzu mahukuntan birnin na New York ba su tabbatar da sahihancinta ba.