An kai sabbin hare-hare a ƙasar Masar | Labarai | DW | 20.07.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kai sabbin hare-hare a ƙasar Masar

Hukumomin tsaro sun ce wasu mutane ɗauke da makamai sun kai hari a kan wani wurin binciken da ke kan iyaka da Libiya.

Harin wanda aka kai a Wadi al Gadid da ke kan iyaka tsakanin Sudan da Libiya da kuma Masar ya yi sanadiyyar mutuwar sojoji 21 kana wasu huɗu suka jikkata. Hukumomin sun ce masu fautaucin miagun ƙwayoyi ne suka kai shi

To amma a cikin wata sanarwa da ya bayyana wani kakakin rundunar sojojin ƙasar, ya ce masu gwagwarmaya ke da alhaki. Sannan kuma ya ƙara da cewar maharan sun jefa wata roka a kan wani rubun ajiyar makamai wanda ya fashe. Wannan shi ne hari irinsa na biyu da aka kai a kan wannan cibiya a cikin wata guda.

Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman