An kai harin bam a Potiskum | Labarai | DW | 03.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kai harin bam a Potiskum

Mutane akalla hudu ne ake zaton sun sheka lahira yayin wannan harin da ya gudana a jihar Yobe da ke yankin Arewa maso gabashin Najeriya.

Wani dan kunar bakin wake ya tayar da bam dake jikinsa a garin Potiskum na jihar Yobe, yayin da wasu Musulmi mabiya mazhabar Shi'a ke yin zanga-zangar lumana. Shaidun gani da ido suka ce sun ji karar fashewar wani abu mai karfin gaske, tare da ganin mutane a kwankwance. Wannan ya zo ne a lokacin da 'yan Shi'ar ke yin muzahara ta Ashura inda aka yi wa Iman Hussaini Jikan Annabi kisan gilla.

Wani da ya gane ma idanunsa, ya bayyana wa wakilin DW na Gombe cewa ya ga gawarwaki hudu da idanunsa da kuma gawar wani da suke zaton shi ne dan kunar bakin waken. Jami'an tsaro suka kwashe wadanda suka jikata da dama zuwa asibiti. Sai dai kuma ya zuwa yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai wannan hari.

A yammacin jiya Lahadi ma dai wasu mutane dauke da ababe masu fashewa sun kai hari a wani gidan kaso na Koton- Karfe dake tsakiyar kasar ta Najeriya inda suka yi sanadiyar tserewar 'yan kaso akalla 50 a cewar Emmanuel Ojukwu kakakin 'yan sandan Najeriya.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe