An kai harin a wani otel a Mali | Labarai | DW | 07.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kai harin a wani otel a Mali

Wasu mutane dauke da makammai sun kai hari da safiyar wannan Jumma'a a Hotel Byblos da ke birnin Sevare a nisan kilo-mita 620 a arewacin Bamako babban birnin kasar Mali.

Shi dai otel din na Byblos shi ne wanda akasarin ma'aikatan samar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a kasar ta Mali ke halarta, inda kawo yanzu aka samu rasuwar mutum daya a cewar wata majiyar tsaron kasar. Mutanen da ba a tantance ba sun kai harin ne a wannan otel da ke bisa hanya mai zuwa filin jirgin saman birnin na Sevare, inda kawo yanzu dakarun kasar ta Mali suka yi wa wajen tsinke a kokarin da suke na dakile wannan hari.

Wasu shaidun gani da ido na ganin cewa harin wani yunkurin sace mutane ne.