An kai hari kan jami′an tsaron Somaliya | Labarai | DW | 24.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kai hari kan jami'an tsaron Somaliya

Masu bai wa dakarun Somaliya daga hadaddiyar Daular Larabawa sun tsallake rijiya da baya lokacin da aka kai hari a birnin Mogadishu

Wani harin kunar bakin wake da mota kan jami'an tsaron kasar Somaliya ya yi sanadiyar hallaka mutane uku da suka hada da fararen hula, yayinda wasu suka samu raunika. Rahotanni sun ce an nemi kai harin kan masu horas da dakarun kasar.

Shaidun gani da ido sun ce lamarin ya faro lokaci maharin a cikin mota ya kara da motar da take dauke da jami'an tsaro a birnin Mogadishu fadar gwamnatin kasar. Kungiyar 'yan ta'adda ta al-Shabaab take kai hare-haren a kasar ta Somaliya mai fama da tashe-tashen hankula.