1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kai hari Amirka da mota

November 22, 2021

Jami'an 'yan sanda a Amirka sun ce kimanin mutane 20 ne ciki har da yara suka jikkata bayan da wata mota ta kutsa cikin dandazon masu faretin kirismeti a jihar Wisconsin. 

https://p.dw.com/p/43JuW
USA Waukesha, Wisconsin Auto rast in Parade
Hoto: Mike De Sisti/Milwaukee Journal-Sentinel via AP/picture alliance

Tuni dai jami'an suka kama wanda ke da alaka da harin a birnin Waukesha, yayin hukumar leken asirin Amirka FBI ta fara bayar da gudunmawarta. Kazalika ita ma fadar White House ta fara nazari kan harin da har yanzu ba a tabbatar da ko na ta'addanci ba ne.

Kawo yanzu dai hukumomi sun bayar da alkalumman mutuwar mutum biyar a harin.