1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kashe mutane a taron Maulidi a Kabul

Abdul-raheem Hassan MNA
November 20, 2018

Hukumomin kasar Afghanistan sun tabbatar da mutuwar sama da mutane 40 tare da jikkata wasu 70, bayan da dan kunar bakin wake ya tarwatsa bam cikin dakin taron tunawa da ranar haihuwar Annabi.

https://p.dw.com/p/38bkW
Selbstmordattentat in Kabul
Hoto: Reuters/O. Sobhani

An kiyasta cewa sama da mutane dubu daya ne ke cikin dakin taron da harin ya auku, sai dai babu wata kungiya da ta dau alhakin kai wannan harin kawo yanzu.

Hukumomi a kasar Afghanistan dai sun tabbatar da mutuwar sama da mutane 40 tare da jikkata wasu 70, bayan da dan kunar bakin wake ya tarwatsa bam cikin dakin taron tunawa da ranar haihuwar Annabi Mohammad, tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi.

Harin shi ne cikamakin hari 20 mafi girma a birnin Kabul cikin wannan shekara kadai, inda aka kiyasta rayukan mutane 490 sun salwanta yayin da sama da mutane 930 suka jikkata.

Kwanaki kalilan kamin wannan hari jami'in Amirka a kasar Afganistan Zalmay Khalilzad ya bayyana fatan cimma yarjejeniyar zaman lafiya da zai kawo karshen yakin shekaru 17 gabannin zaben shugaban kasar a watan Afirilun shekarar 2019.