Mutane shida sun mutu a harin cibiyar G5 Sahel a Mali
June 29, 2018Talla
Wata majiyar tsaro kaar ta Mali ta ce wani dan kunar bakin wake ne ya soma tayar da jigidar bama-baman da ke a jikinsa a lokacin da sojoji suka yi kokarin hana masa shiga cikin barikin sojan kafin daga bisani sauran maharan su buda wuta kan sojojin ta G5 Sahel da ke a garin Sevare na tsakiyar kasar ta Mali.
Sai dai rahotanni na cewa ya zuwa yanzu kura ta lufa sai dai an kawo daukin karin sojoji a birnin. Wannan shi ne karo na farko da aka hari hedikwatar rindunar ta G5 Sahel da ta hada kasashen Mali, Burkina Faso, Nijar, Moritaniya, da Tchadi da nufin kawar da kungiyoyin 'yan ta'adda daga yankin na Sahel.