An kai hare-hare a ƙasar Masar | Labarai | DW | 02.04.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kai hare-hare a ƙasar Masar

Hukumomin tsaro a sun ce wani janar na 'yan sanda ya rasa ransa a sakamakon fashewar wasu abubuwan guda biyu a birnin Alƙahira.

Abubuwan guda biyu waɗanda suka yi bindiga a wani wurin fakewar 'yan sandar,daf da kofar shiga jami'ar birnin Alƙahira, sun kuma raunata mutane guda biyar a ciki har'da wani janar ɗin na 'yan sanda. Tun bayan faɗuwar gwamnatin shugaban ƙasar Mohammed Mursi ake ci gaba da kai hare-haren a ƙasar ta Masar.

Wannan hari na baya-baya nan, ya zo ne kwanaki kaɗan bayan tsohon jagoran sojojin ƙasar Aabdel Fattah Al-Sisi ya tabbatar da takarasa a zaɓen shugaban ƙasar da za a yi a cikin watan Mayu da ke tafe.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu