An kafa sabuwar majalisar ministocin Mali | Labarai | DW | 16.12.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kafa sabuwar majalisar ministocin Mali

Fira minista Diongo Cissoko ya baiyana sabin membobin gwamnatinsa wacce ke da wakilai 29

Sabon fira ministan ƙasar Mali Diongo Cissoko wanda sojoji suka naɗa a makon jiya bayan da suka tilasa wa tsohon fira ministan Cheik Modibo Diarra yin marabus,ya baiyana sunnayen sabin ministocin gwamnatinsa a gidan telbijan na ƙasar.

Majalisar ministocin mai menbobi 29 ta haɗa da wasu sojoji na kusa da kaptain Amadou Haya Sanogo.Ƙasashen duniya masu neman ganin an warware matsalar da ƙasar ta samu kan ta a ciki,sune suka tilasawa sabon fira minista kafa gwamnatin haɗin kan ƙasa domin ƙalubalantar yan tawayen da ke riƙe da yankin arewacin ƙasar sama da watanni tara.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman