An kafa sabuwar gwamnatin hadin kan kasa a Libya | Labarai | DW | 19.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kafa sabuwar gwamnatin hadin kan kasa a Libya

A ranar Talatar nan ce gwamnatin hadin kan kasar Libya data samu ta goma shin Majalisar dinkin duniya ta bayyana kafuwar ta a karkashin wata yarjejeniyar da zata kawo karshen yawan zub da jinin da kasar take fuskan ta.

Tun dai a kwanakin baya ne majalisar dinkin duniya ta bukaci ‘yan majalisar kasar dasu amince da kafa sabuwar gwamnatin, wacce kuma Fayez al-Sarraj hamshakin attajiri nan ya ke ma jagoranci.

Kazalika a nasa bangaren ministan harkokin wajen Libyan Mohammed Al-Dairi cewa yake.

kafa gwamnatin hadin kan kasar libyan yana da matikar mahimanci musamman ga al'umomin kasa da kasa a dai-dai lokacin da suka yi mana nuni da cewar sai mun yi hakan za a janye mana takunkumi da suka hada da makamai ta yadda za mu cigaba da yakar ta'addanci.

Tun dai a shekara ta 2011 kasar Libyan ta tsunduma cikin rikita- rikitar siyasa tare da zubar da jini tsakanin bangarori biyu da basa ga muciji da juna sakamakon hambarar da Mamman Gadafi a gadon mulkin kasar.