An kafa sabuwar gwamnati a Masar
July 16, 2013An naɗa sabuwar gwamnatin ne wadda aka ƙaddamar da bikin rantsar da sabbin manbobinta a gaban shugaban gwamnatin wucin gadi Adly Mansur da fira mistan Hazam Belblawi; da kuma sauran shugabannin sojin da suka kifar da gwamnatin Muhammad Mursi.
Matsayin ministan tsaro ya tsaya ga janar Abdel Fatah Al-Sisi mutumin da shi ne ƙusa a juyin mulkin da aka yi a farkon wannan wata wanda kuma aka naɗa shi muƙadashin shugaban gwamnatin. Yayin da Nabil Fahmy tsohon jakadin ƙasar a Amirka ya zama minsitan harkokin waje, kana na kuɗi aka miƙa shi ga wani msanin tattalin arziki da ke a Bankin Duniya Ahmad Galal. A karon farko an naɗa mata guda uku a cikin sabuwar gwamnatin.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Zainab Mohammed Abubakar