An kafa sabuwar gwamnati a Libiya | Siyasa | DW | 01.11.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

An kafa sabuwar gwamnati a Libiya

Bayan tsawon makonni ana mahawara da cece kuce, majalisar dokokin Libiya ta amince da sabuwar majalisar ministocin gwamnatin Priminista Ali Zeidan.

Hakan ya biyo bayan ƙuri'un da 'yan majalisar suka ƙaɗa a larabar nan, inda mafi rinjaye suka amince. Zaɓen dai ya fuskanci jinkiri na yini guda, sakamakon masu zanga-zangar ɓacin rai da ya mamaye harabar majalisar.

" Na zartar da bada muhimman ma'aikatu wa 'yan takara masu zaman kansu, kamar ma'aikatar shari'a, harkokin kuɗi, tsaro da cikin gida. Bayan hakan, ina tunanin cewar ya zamanto dwajibi kuma a samu ma'aikatar yaɗa labarai".

Waɗannan su ne kalamai da priminista mai sassaucin ra'ayi Ali Zeidan ya gabatar gabanin kaɗa ƙuri'un, bayan kwan da sanin cewar jerin sunayen da ya gabatar zasu samu karɓuwa tsakanin 'yan majalisar. A farkon watan Oktoba ne dai, mai barin kujerarsa ya gaza cimma samun nasarar kafa gwamnati a libiya.

National Kongress wählt Präsident

Majalisar dokoki a Tripoli

Kazalika shima dai sai da aka kai ruwa rana daya hadar da zanga zangar adawa da ɓacin rai na ɗaruruwan 'yan Libiyan a harabar majalisar dokokin dake Tripoli a ranar talata, waɗanda suke korafin cewar, akwai wasu daga cikin sunayen ministocin dake da alaka da tsohuwar gwamnatin Gaddafi. Bayan haka kuma sun bukaci a kara yawan 'yan asalin birnin Tripoli mukaman ministoci.

Hakan dai na bayyana yadda Libiyar ke fuskantar banbancin ra'ayi tsakanin lardunan ƙasar uku. Abun da kuma ake ganin zai ci gaba da taka rawa a harkokin siyasar wannan ƙasa da har yanzu ke fuskantar barazanar tashe tashen hankula. Ko a ranar ta laraba dai ɗaruruwan masun zanga-zanga sun nemi kutsawa zuwa cikin harabar majalisar wakilan ƙasar alokacin da ake kada ƙuri'u akan sabuwar majalisar ministocin, amma jami'ian tsaro sun cimma hanasu shiga. Sai dai an cimma gudanar da zaɓen cikin lumana da maraicen larabar. Majalisar dai ta ƙunshi wakilai 200 amma 132 ne kawai suka halarci zaɓen.

Sakamakon zaɓen dai na nuni da cewa 'yan majalisa 105 ne suka amince da jerin sunayen sabbin ministocin, ayayinda tara suka yi adawa, kana wasu 18 suka ƙi kada ƙuriunsu.

Majalisar ministoci 29 da mataimakan priminista uku dai, suna wakiltan dukkan ɓangarori na siyasa dake taka rawa a Libiya, da suka hadar da gamayyar jam'iyyar masu sassaucin ra'ayi da masu ra'ayin addinin Islama.

Proteste Libyen/ Tripolis

Masu gangamin adawa

Gwamnatin Zeidan dai na bukatar amincewar majalisar wakilan domin haye ƙaragar mulki. Gwamnatinsa ta rikon kwarya zata mayar da hankali kan tabbatar da tsaro a wannan kasa mai albarkatun man petur , inda kuma har yanzu akwai mayaƙan sa kai da suk ajiye makamai, tun bayan kifar da gwamnatin marigayi Muamar Gaddafi.

Mai magana da yawun majalisar wakilan Omar Hmaidan ya fada wa taron manema labaru a Tripoli cewar, akwai ayar tambaya har yanzu akan wasu ma'aikatu, amma sun amince dasu, saboda basa muradin dakatar da gwamnati daga tafiyar da lamuranta. Waɗannan ma'akatu acewar Omar sun haɗar da na cikin gida, lamuran addinai, na harkokin mai , ƙananan hukumomi dana al'amuran ketare.

Priminista Zeidan dai ya kasance tsohon jami'in diplomasiya mai sukar gwamnatin Gaddafi bayan watsi da ita da ya yi a shekatrun 1980s. Wanda a yanzu haka zai jagoranci Libiya, a yayin da majalisar wakilai da aka zaɓa a watan yuli zata zartar da doka tare da taimaka wajen yin sabon kundin tsarin mulki, wanda al'ummar ƙasar zasu ƙaɗa ƙuri'ar raba gardama akai a shekara mai zuwa.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Umaru Aliyu