1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Italiya ta yi sabuwar gwamnati

Gazali Abdou Tasawa
September 4, 2019

A Italiya an kafa sabuwar gwamnati wata daya bayan barkewar rikicin siyisar da ya kai ga rosa gwamnatin kawance ta Firamnista Giuseppe Conte bayan ficewar jam'iyyar masu kyamar baki ta Matteo Salvini daga cikin kawancen.

https://p.dw.com/p/3P19M
Italiens Präsident Mattarella trifft Premierminister Conte im Quirinal Palace in Rom
Hoto: Reuters/F. Ammendola

A kasar Italiya an kafa sabuwar gwamnati a wannan Laraba wata daya bayan barkewar rikicin siyisar da ya kai ga rosa gwamnatin kawance ta Firamnista Giuseppe Conte bayan ficewar jam'iyyar masu kyamar baki ta Matteo Salvini daga cikin kawancen.

Bayan ganawa da Shugaban kasar ta Italiya Sergio Mattarella a wannan Laraba inda ya kaddamar da shi a kan mukaminsa Firamnista Conte wanda ya kulla sabon kawance da jam'iyyar M5S ya kafa sabuwar majalisar ministocinsa mai mambobi 21 da suka hada da mata bakwai da kuma maza 14.

 Firamnista Conte ya mika mukamin ministan kudi na kasar ga Roberto Gualtieri mamba a jam'iyyar Democrate kana shugaban hukumar kula da harakokin tattalin arziki ta Kungiyar EU, Luigi Di Maio na jam'iyyar M5S ya samu mukamin ministan harakokin waje a yayin da Luciana Lamorgese tsohuwar mukaddashiyar gwamnati ta birnin Milan ta tashi da mukamin ministan cikin gida.