An kafa dokar ta-ɓaci a faɗin ƙasar Masar
August 14, 2013Ƙashen duniya sun yi Allah wadai da matakin yin amfani da ƙarfi wanda sojan ƙasar Masar suka yi, don tarwatsa magoya bayan Muhammad Mursi. Firaministan ƙasar Turkiya Raccip Tayyip Erdogan, ya yi ƙira ga ƙasa da ƙasa, lallai su dau mataki kan mahuntan ƙasar ta masar, wadanda suka fara yin amfani da ƙarfi kan sansanin mutanen da basa ɗauke wani makami. Kawo yanzu dai ƙasashen Birtaniya, Jamus da Faransa na daga cikin wadanda suka yi Allah wadai da mataki, inda ita su kuwa ƙasashen Iran da Qatar suka yi kakkausar suka bisa matakin sojojin na Masar. Sakatare janar na MDD Ban Ki-moon, ya bukaci da hukumomin jami'an tsaron Masar dai bayan matakin da suka dauka, aƙalla mutane 124 suka mutu, wasu da dama suka jikkata, yayinda kuma aka tsari wani ƙusa a kungiyar yan uwa musulmai, ta Muslim Brotherhoods. An kuma kafa dokar ta ɓaci na tsawon wata guda a fadin ƙasar, abinda ke nuna cewa an haramta duk wata zanga-zanga.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Umaru Aliyu
RTR