An kafa dokar hana fita a jihar Yobe a Najeriya
October 22, 2012Gwamnatin jihar Yobe da ke a yankin arewa maso gabashin Tarayyar Najeriya ta kafa dokar hana yawo a garin Potiskum mai nisan kilomita ɗari daga Damaturu fadar gwamnatin jihar, daga ƙarfe huɗu zuwa karfe bakwai na safe, domin shawo kan matsalar tsaro da ke addabar garin a ‘yan kwanakin nan. Wata sanarwa da gwamnatin ta fitar ta bayyana cewa ta ɗauki wannan mataki ne bayan wani taro da aka gudanar da masu kula da tsaro domin kawo ƙarshe hasarar rayuka da dukiyoyi da ake yi a garin sanadiyyar tashin hankali da hare-hare da ake kaiwa. Sanarwar ta kuma bukaci da kowa ya zauna gida a dai-dai lokacin da wannan doka ta fara aiki ,tare da neman jama'a su taimaka wa jami'an tsaro a ayyukan su na wanzar da zaman lafiya.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mohammad Nasir Awal