An kafa dokar hana cin kasuwannin dare a Yola | Siyasa | DW | 19.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

An kafa dokar hana cin kasuwannin dare a Yola

'Yan kasuwa dake hada-hada cikin dare a jihar Adamawa na kokawa kan matakin dakatar da harkokinsu da gwamnati ta yi, saboda dalilan tsaro.

Da yammacin ranar Laraba ne gwamnatin ta jihar Adamawa ta sanar da matakin dakatar da duk wasu hada-hada na saye da sayarwa cikin dare a fadar jihar. Hakan kuwa ya biyo bayan wata ganawa ce da aka yi ranar Larabar tsakanin gwamnati da jami'an tsaro a birnin Yola. Wannan mataki dai, kamar yadda aka sanar, ya fara aiki ne nan da nan tun da aka gabatar dashi. A karkashinsa, gwamnatin ta hana harkokin kasuwanci cikin dare tun daga karfe shidda na yamma a ko wace rana, har sai gwamnatin ta ga dacewar lokacin da ya kamata a kawar da wannan doka.

Daruruwan jama'a ake sa ran wannan mataki zai shafi tattalin arzikinsu, musamman wadanda suka dogara rayuwarsu da sana'oi ko kasuwaninsu cikin dare. Saboda haka ne mutane da yawa da abin ya shafa suka fara kokawa, duk kuwa da alfanun da gwamnati tace yana tattare da daukar matakin na hana kasuwanci cikin dare da bukatar samun zaman lafiya da kare lafiyar jama'a. Na zanta da wasu masu hada-hadar cikin dare a fadar ta jihar Adamawa. Wani mai suna James yake cewa:

Gaskiya wannan abu zai dameni. Ka gani mutane da yawa suna zuwa nan suna sayen kati. Da yawa suna karar cewar ba kudi, ba aiki, gashi kuma mutane da yawa nake taimakonsu a iyalina. Da can ina samun dan wani abu amma ba mai yawa ba, to yanzu ma babu gaba daya.

Wani mutum kuma mai suna Williams yayi korafin cewar:

"Kamar mu yan kananan yan kasuwa, sai da dare ne muk dan samun abin da muke rufa ma kanmu asiri, mu rika biyawa yaranmu makaranta, muna dai iya kokarinmu. Ka ga idan ya zama wannan harka babu ita, hakan ya zama mana abin damuwa ne".

Shi kuma wani mai sana'ar gyaran kwamputa, wato injuna masu kwakwara dake kiran kansa Dr. Sabuwar Computer cewa yayi:

"Zai iya shafan sana'ata, saboda ba ma ni kadai ba, wasu mutane da dama sai cikin dare ne sukan sami abin da za su ci. Daga wurinsu mukan sami dan wani abu. Idan suka sami kudi za ka ga mun dan wani wani abu. Idan da rana muka dan sami wani abu, sai mu zagaya mu sayi wasu abubuwa a wurin masu kasuwar dare".

Nigeria Adamawa Ahmad Sajoh Informationsminister

Kwamishinan yada labarai na jihar Adamawa, Ahmed Sajoh

Sai dai fa gwamnatin ta Adamawa wadda ta tabbatar da kafa wannan doka, tace da kyakkyawar manufa aka yi hakan. Alhaji Ahmed Sajoh, shine kwamishinan yada labarai na gwamnatin ta Adamawa.

"Yace wadannan sabbin matakai da muka dauka bisa shawarwari na jami'an tsaro, ya shafi dukkan kasuwanni da ake ci da daddare, saboda sai kana raye ne za ka ci kasuwa ko zuwa wurare da ake shakatawa idan yadda tayi. Shine muka ce to a dan kwana daya ko biyu a dakatar mu gani. Mutanen nan suna neman inda ake da taruwar jama'a ne, amma idan kana da dan shagonka a kofar gida, ko wata tana tuya a rumfarta sun san cewar ba za su iya yin barazana ga rayuwa da yawa ba idan suka kai masu hari. Dokar dai ta shafi birnin Yola ne kawai, amma a bisa shawarar jami'an tsaro, idan suka ce za su aiwatar da dokar a jihar Adamawa baki daya ba za mu hana su ba. Idan kuma suka takaita daga fadar jihar ne kawai, nan ma ba za mu hanasu ba".

Masu nazarin al'amuran yau da kullum a nan Adamawa sun fi kalllon tasirin wannan mataki fiye ma da koke-koken jama'ar da wannan dokar ta shafa, ganin cewar ko baya ma an yi zaman dokar-ta-baci a fadin jihar, kuma hakan bai hana ci gaba da rayuwa ba.

Sauti da bidiyo akan labarin