An ja kunnen 'yan siyasan Madagaskar
August 6, 2013Ƙungiyar Tarayyar Turai ta ja kunnen dukkan waɗanda ke kawo cikas ga gudanar da zaɓe a ƙasar Madagaska, inda aka basu nan da makwannin biyu da su warware rikicin siyasar ƙasar. Kantomar harkokin ƙetare a ƙungiyar EU Catherine Ashton ce ta bada sanarwar cewa, duniya ba za ta lamunta a ci gaba da hana ruwa gudu don komawar ƙasar mulkin demokradiyya ba. Tun dai bayan juyin mulkin da ya ɗora Andry Rajoelina kan mulki a shekara ta 2009 aka kasa gudanar da zaɓe bisa rarrabuwar kawunan 'yan siyasa. Masu shiga tsakani daga ƙungiyar Tarayyar Afirka sun bada shawar cewa 'yan takara uku da suka hana ruwa gudu, wato shugaba mai ci Andry Rajoelina da Lalao matar Marc Ravalomanana wanda Rajoelina ya karɓi mulki a hannunsa da kuma Didier Ratsiraka da cewa duk su ajiye takaransu ko a samu lafawar al'umura, inda yanzu komai ya dagule wa 'yan siyasan, amma duk 'yan takarn kowa ya yi ƙememe.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Yahouza Sadisou Madobi