1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An harbo balan-balan leken asiri na Chaina

Abdoulaye Mamane Amadou
February 5, 2023

Ma'aikatar tsaron Amirka ta kakkabo balan-balan da ya jima yana shawagi a sararin samaniyarta, sai dai hukumomin Chaina na cewa za su dauki matakan da suka dace

https://p.dw.com/p/4N7Hb
NOT the downed balloon! *** USA Kingstown, N.C. | mutmaßlicher Spionage-Ballon aus China
Hoto: Brian Branch/AP Photo/picture alliance

Chaina ta nuna rashin jin dadi kan abinda ta kira amfani da karfi wajen kakkabo balan-balan din kasar da Amirka ta zarga da lekon asiri a wani bangare na sararin samaniyarta.

Wani jiragen yakin Amirka samfarin F-22 ne dai ya kakkabo balan-balan din da ya shafe tsawon kwanaki yana shawagi a sararin samaniyar Amirkar a daidai gabar tekun Carolin ta Kudu, bayan umarnin da mahukuntan Amirka suka bayar na daukar matakan da suka dace kan shawagin blan-blan din, kana a na cigaba da tattara ragowar baraguzan na'urar da Amirkar ta zargi Chaina da kokarin yi mata lekon asiri.

Wannan lamarin dai ya kara zafafa takaddamar diflomasiyyar da ta jima tana tsami a tsakanin kasashen biyu, wanda har ta kai ga babban sakataren harkokin wajen Amirka Antony Blinken, dage wata ziyarar kwanaki biyu da zai kai a Beijing.