1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An haramta zanga-zanga a Hong Kong

Zulaiha Abubakar
August 30, 2019

Jami'an tsaro a yankin Hong Kong sun cafke wasu 'yan majalisar dokoki biyu masu rajin kare dimukuradiyya bisa zarginsu da haifarwa da 'yan sanda tsaiko a ayyukan tsaro.

https://p.dw.com/p/3Om7v
Hongkong Protest Polizei
Hoto: Reuters/K. Pfaffenbach

Da farko jami'an tsaron sun kame Joshua Wong Hong 'dan gwagwarmaya bisa zarginsa da karya umarnin gwamnati na haramta zanga-zangar da ta dauki tsawon watanni hudu ana fafatawa duk da cewar  hukumomi sun gargadi masu boren game da kiran sabuwar zanga-zanga a gobe Asabar. Kasashen ketare da kungiyoyi sun zargi China da hannu cikin wannan rikicin siyasa da yankin na Hong Kong ya tsunduma.